1 Kings 8:64 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ سَرْكِے يَكُمَ كٜىٰٻٜىٰ ڢِيلِنْ دَيَكٜىٰ أَغَبَنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ أَوُرِنْ نٜىٰ يَمِيڧَ هَدَايُنْ ڧُواْنَاوَا دَ نَغَرِ دَ كِڟٜىٰنْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ، غَمَا بَغَدٜىٰنْ تَغُلَّرْ دَيَكٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ يَا كَاسَ سُواْسَيْ دَ ذَاعَيِ دُكَنْ وَطَنَّنْ هَدَايُ عَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.