1 Samuel 1:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
هَنَّةُ كُوَ تَأَمْسَ «أَعَ، رَنْكَيَدَطٜىٰ، بَهَكَ بَنٜىٰ؞ نِے مَثٜىٰ ثٜىٰ مَيْ بَڧِنْ ثِكِ سُواْسَيْ؞ بَنْشَا ضُوً إِنَبِے كُواْ وَنِ أَبُ مَيْسَا بُغُوَبَ، عَمَّا إِنَ بَيَّنَ ذُوثِيَاتَ نٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.