1 Samuel 1:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk sa’ad da rana ta kewayo don Elkana yă miƙa hadaya, yakan ba da kashin nama ga matarsa Feninna da dukan ’ya’yanta maza da mata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ لُواْكَثِنْ دَ عٜىٰلْكَنَ يَمِيڧَ هَدَايَ، يَكَنْ بَا مَاتَرْسَ ڢٜىٰنِينَّتُ دَ دُكَنْ یَیَنْتَ مَظَا دَ مَاتَا كُواْوَ نَاسَ رَبُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo.