1 Samuel 1:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ ڟُواْكَنَرْ تَاثِيغَبَ كُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا؞ كُواْوَنٜىٰ لُواْكَثِنْ دَ هَنَّةُ تَتَڢِے غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ ڢٜىٰنِينَّتُ تَيِ تَڟُواْكَنَرْتَ حَرْ تَيِ تَكُوكَا تَڧِ ثِنْ عَبِنْثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci.