1 Samuel 10:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi a dā suka gan shi yana annabci tare da annabawa, sai suka tambayi juna, suka ce, “Me ya faru da ɗan Kish? Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَ سَنْشِ كَاڢِنْ وَنَّنْ يَڢَرُ، سُكَغَ يَنَ أَنَّبْثِ تَرٜىٰدَ أَنَّبَاوَا، سَيْ مُتَنٜىٰنْ سُكَثٜىٰ وَجُونَ «شِنْ، مٜىٰيَسَامِ طَنْ كِشْ؟ طَالُوتَ شِے مَا أَنَّبِے نٜىٰ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?”