1 Samuel 10:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ كَرَبُ دَنِے يَوْ، ذَاكَ سَدُ دَ مَظَا بِيُ كُسَدَ كَبَرِنْ رَحِيلَةُ أَ ظٜىٰلْظَ عَ إِيَاكَرْ يَنْكِنْ بِلِيَامِنُ؞ مُتَنٜىٰنْ ذَاسُ ڢَطَا مَكَ ثٜىٰوَ أَنْسَامِ جَاكُنَنْدَ كَڢِتَ نٜىٰمَ؞ يَنْذُ بَابَنْكَ يَبَرْ دَامُوَ عَكَنْسُ، يَڢَارَ دَامُوَ عَكَنْكُ، يَنَ تَتَمْبَيَ يَنَ ثٜىٰوَ «تُواْ، مٜىٰ ذَنْيِ غَمٜىٰدَ طَانَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yau, sa'ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’