1 Samuel 11:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
جَمَعَ غَبَاطَيَ سُكَ تَڢِے غِلْغَلْ؞ عَثَنْ غِلْغَلْ سُكَ تَبَّتَرْ دَ طَالُوتَ سَرْكِے أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ سُكَ مِيڧَ هَدَايُ نَڠَرَنْ زُمُنْثِ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ طَالُوتَ كُوَ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَيِ ڢَضٍ ثِكِ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jama'a duka kuwa suka nufi Gilgal, suka yi wa Saul wankan sarauta a gaban Ubangiji. Suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama. A can kuwa Saul tare da dukan mutanen Isra'ila suka yi murna ƙwarai.