1 Samuel 11:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَكَشٜىٰ شَانُنْسَ بِيُ، يَرَرَّبَ نَامَنْسُ ڟُواْكَ ڟُواْكَ، يَبَا یَنْ عَيْكَ سُكَيْسُ كُواْعِنَ عَيَنْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ يَثٜىٰ دُكْ عِنْدَ سُكَ تَڢِے سُنُونَ نَامَنْ سُثٜىٰ «دُكْ وَنْدَ بَيْ ڢِتَ يَغُواْيِ بَايَنْ طَالُوتَ دَ سَمَٰعِيلَ عَيَاڧِ بَ، حَكَ ذَاعَيِ دَ شَانُنْسَ؞» دَجِنْ وَنَّنْ، ڟُواْرُواْ دَغَ وُرِنْ يَهْوٜىٰهْ يَاكَامَ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُواْسَيْ؞ سَيْ دُكَنْ مَظَا سُكَ ڢِتُواْ غَبَاطَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko'ina a ƙasar Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama'ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!” Jama'a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.