1 Samuel 13:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَمَٰعِيلَ يَتَاشِ دَغَ غِلْغَلْ يَيِ تَڢِيَرْسَ؞ طَالُوتَ كُوَ يَڧِرْغَ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ أَ غِبٜىٰيَ عَيَنْكِنْ ذُرِيَرْ بِلِيَامِنُ، سَيْيَسَامِ طَرِے شِدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sama'ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.