1 Samuel 13:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَنْ غَنْغَرَ ذُوَا وُرِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا دُواْمِنْ سُڠَرَ بَاكِنْ غَرْمَرْسُ دَ ڢَرْتَنْيَرْسُ دَ غَاتَرِنْسُ دَ لَوْجٜىٰنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka kowane Ba'isra'ile yakan gangara zuwa Filistiyawa domin ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa,