1 Samuel 14:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, waɗanda suke cikin sansanin da waɗanda suke fili, har da waɗanda suke waje, da kuma waɗanda suke kai hari, ƙasa ta girgiza. Allah ne ya kawo wannan rikicewa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڟُواْرُواْ يَكَامَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا دَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَثِكِنْ سَنْسَنِنْ يَاڧِ دَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ وَجٜىٰ، حَرْ مَا دَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ أَ ڢِيلِ دَ كُمَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ كَيْ هَرِ؞ دُكَنْسُ سُكَجِڟُواْرُواْ سُواْسَيْ حَرْ سُكَ ضِكِثِے؞ عَكَيِ ضَوَرْ ڧَسَا؞ اللَّهْ نٜىٰ كُوَ يَكَٰوُاْ وَنَّنْ ضِكِثِيوَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.