1 Samuel 14:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Shawulu ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ku ƙidaya mayaƙa ku ga wane ne ba ya nan.” Da suka ƙirga sai suka tarar Yonatan da mai ɗaukan makamansa ba sa nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَثٜىٰ وَمُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰدَشِ «كُڧِرْغَ سُواْجُواْجِنْ دُواْمِنْ أَغَ وَنْدَ بَايَ نَنْ؞» دَ عَكَيِ ڧِرْغٜىٰ سَيْ عَكَ غَانٜىٰ يُواْنَتَنْ دَ مَيْ رِڧٜىٰ مَسَ كَايَنْ يَاڧِنٜىٰ بَاسَ نَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan.