1 Samuel 14:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi Filistiyawan zuwa sansanin yaƙinsu, suka juya, suka goyi bayan Shawulu da Yonatan sa’ad da yaƙin ya taso.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِبْرَنِيَاوَنْ كُوَ دَ دَا مَا سُكٜىٰ تَرٜىٰدَ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ كُمَبِے ڢِلِسْتِيَاوَنْ ذُوَا سَنْسَنِنْ يَاڧِنْسُ، سُكَ جُويَا سُنَ غُواْيُوانْ بَايَنْ طَالُوتَ دَ يُواْنَتَنْ أَ لُواْكَثِنْ دَ يَاڧِنْ يَتَاسُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra'ilawan da suke tare da Saul da Jonatan.