1 Samuel 14:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dukan Isra’ilawan da suka ɓuya a duwatsu a ƙasar Efraim suka ji labari cewa Filistiyawa suna gudu, sai suka fito suka fafare su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَنْ دَ سُكَ ٻُيَ عَتُدَّنْ يَنْكِنْ ذُرِيَرْ إِڢْرَيِمْ سُكَجِ ثٜىٰوَ سُواْجُواْجِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُنَ غُدُ، سَيْ سُو مَا سُكَ شِغَ يَاڧِنْ دَ ذَاڢِ سُكَ كُواْرِ ڢِلِسْتِيَاوَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su.