1 Samuel 14:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُوَ سُنْ شَا وَهَلَ سُواْسَيْ، غَمَا طَالُوتَ يَيِ ضَنْڟُوَا ثٜىٰوَ «لَعَنَنّٜىٰ نٜىٰ مُتُمِنْدَ يَثِ عَبِنْثِ كَاڢِنْ ڢَاطُوَرْ رَانَ، تُنْ بَنْ يِ رَامُوَا عَكَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنَبَ؞» سَبُواْدَ حَكَ بَابُ سُواْجَنْدَ يَثِ عَبِنْثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.