1 Samuel 14:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo shanu da tumaki a nan, su yayyanka, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Haka nan kowa ya kawo saniyarsa a daren, ya yanka a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَثٜىٰ «كُتَڢِے كُڢَطَا وَسُواْجُواْجِنْ كُواْوَ يَكَٰوُاْ سَانِيَرْسَ دَ تُنْكِيَرْسَ يَيَنْكَ أَدُوڟٜىٰنَّنْ يَثِ؞ كَدَ كُيِ وَ يَهْوٜىٰهْ ذُنُوبِ تَوُرِنْ ثِنْ نَامَ تَرٜىٰدَ جِنِنْ؞» أَ دَرٜىٰنَّنْ كُوَ كُواْوَ يَكَٰوُاْ دَبَّرْسَ يَيَنْكَ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama'a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin.