1 Samuel 14:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu ya ce, “Mu bi gangara mu fafare Filistiyawa da dare mu washe su har gari yă waye, mu kuma karkashe kowannensu, kada mu bar wani da rai.” Suka ce, “Ka yi duk abin da ka ga ya fi maka kyau.” Amma firist ya ce, “Bari mu nemi nufin Allah tukuna.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَثٜىٰ «بَرِ مُغَنْ‌غَرَ مُڢَاطَوَ ڢِلِسْتِيَاوَا دَ يَاڧِ دَ دَرٜىٰنَّنْ، مُكَكَّشٜىٰسُ، مُيِ تَݣُوشِ كَايَنْسُ حَرْ وَايٜىٰوَرْ غَرِ؞ كَدَ مُبَرْ كُواْ طَيَ عَثِكِنْسُ دَ رَيْ!» سُكَ أَمْسَ سُكَثٜىٰ «كَيِ دُكْ أَبِنْدَ كَغَ يَدَاثٜىٰ؞» عَمَّا ڢِرِسْتِ يَثٜىٰ «بَرِ مُتَمْبَيِ اللَّهْ تُكُنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Saul ya ce, “Mu tafi, mu fallasa Filistiyawa da dare har wayewar gari, kada ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira.” Sai suka ce masa, “Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau.” Amma firist ɗin ya ce, “Bari mu yi tambaya ga Allah.”