1 Samuel 14:41 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, “Me ya sa ba ka amsa mini addu’ata a yau ba? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Yonatan, ka nuna mana ta wurin Urim, amma idan laifin mutanen ne ka amsa ta wurin Tummim.” Ba a sami mutane da laifi ba, amma ƙuri’a ta fāɗa a kan Yonatan da Shawulu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَالُوتَ يَيِ أَدُّعَ يَثٜىٰ «يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، مُنَ ضُواْڧُوانْكَ كَنُونَ مَنَ مَيْلَيْڢِے؞» سَيْ عَكَ نُونَ طَالُوتَ دَ يُواْنَتَنْ تَوُرِنْ أَمْڢَانِ دَ عُرِمْ دَ تُمِّمْ، سَوْرَنْ بَعَسَامٜىٰسُ دَ وَنِ لَيْڢِے بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama'a kuwa suka kuɓuta.