1 Samuel 15:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ دَ سَڢٜىٰ سَيْ يَتَاشِ يَنَ نٜىٰمَنْ طَالُوتَ؞ عَكَ ڢَطَا مَسَ ثٜىٰوَ طَالُوتَ يَتَڢِے كَرْمٜىٰلْ، عِنْدَ يَغِنَ وَكَنْسَ أَبِنْدَ ذَاعَ دِنْغَ تُنَاوَا دَشِ؞ دَغَ ثَنْ يَوُثٜىٰ ذُوَا غِلْغَلْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.