1 Samuel 15:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da ’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَالُوتَ دَ سُواْجُواْجِنْسَ سُكَ بَرْ سَرْكِے أَغَغْ دَ رَيْ، تَرٜىٰدَ تُمَكِ مَڢِے ݣَوْ دَ شَانُو دَ یَیَنْ شَانُو دَ یَیَنْ تُمَكِ دَ كُمَ دُكْ أَبِنْدَ يَيِ مُسُ ݣَوْ سُواْسَيْ؞ دُكْ وَطَنَّنْ كُوَ بَسُ كَشٜىٰسُبَ؞ عَمَّا سُنْ كَشٜىٰ دُكَنْ دَبُّواْبِنْ دَسُكٜىٰ مَرَرْ لَاڢِيَ كُواْ مَرَرْ أَمْڢَانِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.