1 Samuel 17:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ كُوَ طَنْ يٜىٰسّٜىٰ نٜىٰ، مُتُمِنْ عٜىٰڢْرَتَ دَغَ بَيْتَلَحْمِ تَيَنْكِنْ يَهُودَ؞ يٜىٰسّٜىٰ كُوَ يَنَدَ یَیَ مَظَا تَݣُوسْ؞ أَ لُواْكَثِنْ دَ طَالُوتَ يَكٜىٰ مُلْكِ، يٜىٰسّٜىٰ يَا رِغَا يَا ڟُوڢَ، شٜىٰكَرُنْسَ كُمَ سُنْيِيَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.