1 Samuel 17:39 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَرَاتَيَ تَكُواْبِنْ طَالُوتَ عَكَنْ رِغَرْ ڧَرْڢٜىٰنْدَ يَسَا، سَعَنً يَيِ ڧُواْڧَرِ يَيِ تَڢِيَ عَمَّا يَكَاسَ، غَمَا بَيْسَابَادَ سَا وَطَنَّنْ كَايَنْبَ؞ سَيْ دَاوُدَ يَثٜىٰ «بَذَنْ عِيَ تَڢِيَ دَ وَطَنَّنْبَ، غَمَا بَنْ سَابَادَسُوبَ؞» سَيْ دَاوُدَ يَتُوٻٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Dawuda ya sa kayan yaƙin, ya rataya takobi, ya fara tafiya, sai ya ji ba zai iya ba, domin bai saba da su ba. Sai ya ce wa Saul, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, gama ban saba da su ba.” Ya kuwa tuɓe su.