1 Samuel 17:41 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمِنْ ڢِلِسْتِيَ شِے مَا يَڢِتُواْ يَنَ غُسُواْوَ ذُوَا وُرِنْ دَاوُدَ؞ مَيْ رِڧٜىٰ مَسَ غَرْكُوَرْ يَاڧِ كُوَ يَنَ تَڢِيَ أَغَبَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bafilisten kuma ya nufo Dawuda, mai ɗaukar masa garkuwa yana gabansa.