1 Samuel 17:46 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَوْ طِنَّنْ يَهْوٜىٰهْ ذَيْبَادَكَيْ أَ هَنُّونَ؞ ذَنْ كَشٜىٰكَ إِنْ يَنْكٜىٰ كَنْكَ؞ يَوْ طِنَّنْ كُمَ ذَنْبَا ڟُنْڟَيٜىٰ دَ نَمُواْمِنْ دَاجِ جِكُنَنْ سُواْجُواْجِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُثِ؞ تَهَكَ دُونِيَا دُكَ ذَاتَ سَنْ ثٜىٰوَ لَلَّيْ أَݣَويْ اللَّهْ عَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila.