1 Samuel 17:47 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُمَ دُكَنْ تَارُوانْ جَمَعَرْ نَنْ ذَاسُ سَنِ ثٜىٰوَ يَهْوٜىٰهْ بَايَ بُڧَاتَ تَكُواْبِے كُواْ مَاشِ دُواْمِنْ يَثٜىٰثِ مُتَنٜىٰنْسَ؞ يَاڧِ نَ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ، كُمَ ذَيْبَادَكُو ڢِلِسْتِيَاوَا أَ حَنُّنْمُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Taron jama'ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da mashi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.”