1 Samuel 18:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ طَالُوتَ يَثٜىٰ وَ دَاوُدَ «غَا یَتَ تَڢَارِ مٜىٰرَبْ؞ ذَنْ بَاكَ عِتَ كَأَوْرَ؞ عَمَّا سَيْدَيْ كَيِمِنِ حِدِمَ دَ ڧَرْڢِنْ حَلِ كَكُمَيِ يَاڧٜىٰ يَاڧٜىٰنْ يَهْوٜىٰهْ ؞» طَالُوتَ يَثٜىٰ حَكَ غَمَا يَنَ تُنَانِ أَ رَنْسَ ثٜىٰوَ «نِے بَذَنْسَا هَنُّونَ إِنْ كَشٜىٰ دَاوُدَ بَ، بَرِ يَمُتُ أَ حَنُّنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar 'yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.)