1 Samuel 18:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْيَثٜىٰ وَكَنْسَ «ذَنْ بَا دَاوُدَ مِكَلْ؞ ذَنْسَا تَذَمَ مَسَ تَرْكُواْ، حَرْ سَيْ يَمُتُ أَ حَنُّنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞» دُواْمِنْ حَكَ سَيْ طَالُوتَ يَثٜىٰ وَ دَاوُدَ سَوْ نَبِيُ «يَنْذُ ذَاكَ ذَمَ مِجِنْ یَتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.”