1 Samuel 18:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَثٜىٰ «كُڢَطَا وَ دَاوُدَ، ‹أَيْ، سَرْكِے بَايَ بُڧَاتَرْ كُطِنْ عَوْرٜىٰ؞ أَبِنْ دَ دَيْ يَكٜىٰ بُڧَاتَ شِينٜىٰ ڢَتَرْ أَذَّكَرِ طَرِے نَ ڢِلِسْتِيَاوَا، دُواْمِنْ يَيِ رَامُوَا عَكَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْ سَرْكِے؞› » وَنَّنْ دَبَرَثٜىٰ دَ طَالُوتَ يَيِ دُواْمِنْ دَاوُدَ يَمُتُ أَ حَنُّنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saul kuma ya ce, “Haka za ku faɗa wa Dawuda, ‘Sarki ba ya so ka ba da sadaki don auren, sai dai ka ba da loɓar Filistiyawa guda ɗari, domin ka ɗauki fansa a kan maƙiyan sarki.’ ” (Saul dai yana so Filistiyawa su kashe Dawuda kawai.)