1 Samuel 18:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَايِنْ دَ طَالُوتَ دَ سَوْرَنْ سُواْجُواْجِنْ سُكٜىٰ كُواْمَ غِدَا بَايَنْدَ دَاوُدَ يَكَشٜىٰ مُتُمِنْ ڢِلِسْتِيَ، سَيْ مَاتَا سُكَ ڢِڢِّتُواْ دَغَ دُكَنْ غَرُضُوً إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ سُمَرَبْثِ سَرْكِے طَالُوتَ؞ سُنَ وَاڧُواْڧِ نَنُونَ ڢَضٍ ثِكِ، سُنَ ضَوَ، سُنَ كَطَ تَمْبُرَ دَ مُواْلُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da sojoji suke komowa gida, bayan da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai mata daga kowane gari na Isra'ila suka fito domin su taryi sarki Saul. Suna raira waƙar farin ciki, suna rawa, suna kaɗa kuwaru da molaye.