1 Samuel 18:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ يَسَا طَالُوتَ يَيِ ڢُشِے سُواْسَيْ، يَثٜىٰ «مَتَ سُنْ ثٜىٰ دَاوُدَ يَكَشٜىٰ دُبُنْ دُبَّيْ، عَمَّا نِے دُبَّيْ كَطَيْ سُكَ بَا نِے؞ مٜىٰ كُمَ يَضَغٜىٰ مَسَ، أَيْ، سَيْ مُلْكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan waƙa ta ba Saul haushi, ya ce, “Sun ba Dawuda dubun dubbai, amma dubbai kawai suka ba ni, me kuma ya rage masa, ai, sai sarauta.”