1 Samuel 19:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَيِ ڧُواْڧَرِ يَكَڢٜىٰ دَاوُدَ دَ مَاشِ دَ بَنْغُواْ عَمَّا دَاوُدَ يَكَوْثٜىٰ؞ سَيْ مَاشِنْ يَوُثٜىٰ يَسُواْكِ بَنْغُواْ حَرْ يَكَڢٜىٰ؞ دَاوُدَ كُمَ يَغُدُ يَكُٻُثٜىٰ دَ دَرٜىٰنَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.