1 Samuel 19:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَالُوتَ يَعَيْكِ مُتَنٜىٰنْسَ ذُوَا غِدَنْ دَاوُدَ سُيِ غَادِنْسَ، دُواْمِنْ سُكَشٜىٰشِ دَ سَڢٜىٰ؞ عَمَّا مِكَلْ مَاتَرْ دَاوُدَ تَثٜىٰمَسَ «يَوْ دَ دَرٜىٰ عِدَنْ بَكَ غُدُ دَ رَنْكَ بَ، غُواْبٜىٰ ذَاكَ مُتُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A daren nan Saul ya aiki manzanni su je gidan Dawuda don su yi fakonsa, su kashe shi da safe. Amma Mikal, matar Dawuda, ta faɗa masa cewa, “Idan ba ka gudu da daren nan ba, gobe za a kashe ka.”