1 Samuel 19:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya tuttuɓe rigunarsa, ya kuma yi annabci a gaban Sama’ila. Ya kwanta tsirara dukan yini da dukan dare. Abin da ya sa ke nan mutane suke cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِمَا يَتُوٻٜىٰ كَايَنْسَ، يَيِ أَنَّبْثِ دَ إِيهُ دَ ضَوَ أَغَبَنْ سَمَٰعِيلَ؞ يَݣُونْتَ ڟِرَرَ دُكَنْ رَانَ دَ دَرٜىٰنَّنْ؞ أَ نَنْ نٜىٰ كَرِنْ مَغَنَ نَنْ يَتَاسُواْ مَيْ ثٜىٰوَ «طَالُوتَ شِے مَا أَنَّبِے نٜىٰ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”