1 Samuel 19:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ يُواْنَتَنْ يَيَبِے دَاوُدَ أَغَبَنْ بَابَنْسَ طَالُوتَ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ! كَدَ كَيِ وَبَاوَنْكَ دَاوُدَ وَنِ لَيْڢِے؞ بَيْ تَٻَيِ مَكَ لَيْڢِے بَ، أَمَيْمَكُوانْ حَكَ دُكَنْ أَبُبُوَنْ دَ يَيِ سُنْ ذَمَ دَ تَيْمَكُواْ ذُوَا غَرٜىٰكَ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.