1 Samuel 2:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْ كَاڢِنْ عَڧُواْنٜىٰ كِڟٜىٰ، مَيْيِ وَڢِرِسْتِ حِدِمَ يَكَنْذُواْ وُرِنْ وَنْدَ يَكَٰوُاْ هَدَايَرْ يَثٜىٰ، «كَبَا ڢِرِسْتِ نَامَ يَغَسَ؞ غَمَا بَذَيْ كَرْٻِ دَڢَڢّٜىٰنْ نَامَ دَغَ غَرٜىٰكَبَ، سَيْدَيْ طَنْيٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”