1 Samuel 2:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu ’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عٜىٰلِ كُمَ يَكَنْ أَلْبَرْكَثِ عٜىٰلْكَنَ دَ مَاتَرْسَ، يَثٜىٰ «بَرِ يَهْوٜىٰهْ يَ أَلْبَرْكَثٜىٰكَ دَ وَطَنْسُ یَیَ دَغَ مَثٜىٰنَّنْ، أَمَيْمَكُوانْ وَنَّنْ يَرُوانْ دَ كُكَ بَا يَهْوٜىٰهْ ؞» بَايَنْ وَنَّنْ عٜىٰلْكَنَ دَ هَنَّةُ سُكَنْ كُواْمَ غِدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.” Bayan wannan sai su koma gida.