1 Samuel 2:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin labari duk abin da ’ya’yansa suke yi wa dukan Isra’ila, da yadda suke lalata da matan da suke hidima a bakin ƙofar Tentin Sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عٜىٰلِ كُوَ يَڟُوڢَ سُواْسَيْ؞ يَنَ كُمَ جِنْ دُكَنْ أَبُبُوَنْ دَ یَیَنْسَ مَظَا سُكٜىٰيِ وَمُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ كُمَ يَدَّ سُكٜىٰ ݣُونَ دَ مَاتَا مَاسُيِنْ حِدِمَ عَڧُواْڢَرْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.