1 Samuel 2:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَا كُمَ ذَاٻِ عِيَلِنْسَ دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ ڧَبِيلُنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُذَمَ ڢِرِسْتُواْثِنَ، سُكُمَيِ حِدِمَ عَبَغَدٜىٰ، سُڧُواْنَ تُرَارٜىٰ، سُطَوْكِ عٜىٰڢُوادْ نَنٜىٰمَنْ نُڢِينَ؞ نَا كُمَبَا كَكَنْكَ دَ عِيَلِنْسَ رَبُوانْسُ دَغَ دُكَنْ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade.