1 Samuel 2:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci, masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Ita da take bakararriya, ta haifi ’ya’ya bakwai amma ita da tana da ’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْدَ أَدَا سُنَدَ عَبِنْثِ سُواْسَيْ، يَنْذُ سُنَيِنْ عَيْكِ نَنٜىٰمَنْ عَبِنْثِ؞ عَمَّا وَطَنْدَ أَدَا سُكٜىٰجِنْ يُنْوَ، يَنْذُ سُنْڧُواْشِ؞ مَثٜىٰنْ دَ دَا بَاتَدَ یَیَ، يَنْذُ تَنَدَ یَیَ بَݣَويْ؞ عَمَّا عِتَ دَ تَكٜىٰدَ یَیَ دَيَوَ، تَبُوشٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci, Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai, Wadda ta haifi 'ya'ya da yawa kuwa ta rasa su duka.