1 Samuel 20:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Dawuda ya gudu daga Nayiwot a Rama ya je wurin Yonatan ya ce, “Me na yi? Wane laifi ne na yi? Ta wace hanya ce na yi wa mahaifinka laifi har da yake neman yă kashe ni?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ دَاوُدَ يَغُدُ دَغَ وُرِنْ ذَمَنْ أَنَّبَاوَا أَ رَمَ ذُوَا وُرِنْ يُواْنَتَنْ؞ يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ نَيِ؟ وَنٜىٰ لَيْڢِے نَيِ؟ وَنٜىٰ ذُنُوبِ نَعَيْكَتَ وَ بَابَنْكَ دَيَكٜىٰ نٜىٰمَ يَطَوْكِ رَيْنَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?”