1 Samuel 20:42 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُواْنَتَنْ يَثٜىٰ وَ دَاوُدَ «كَتَڢِے دَ سَلَمَ، غَمَا مُنْ رِغَا مُنْيِ وَجُونَ ضَنْڟُوَا دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ثٜىٰوَ ‹ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ شَيْدَ ڟَكَانِينَ دَكَيْ دَ كُمَ ظُرِيَاتَ دَ ذُرِيَرْكَ حَرْ أَبَدَا؞› » سَعَنً دَاوُدَ يَتَڢِے، يُواْنَتَنْ كُمَ يَكُواْمَ ثِكِنْ غَرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jonatan ya ce wa Dawuda, “Sai ka tafi lafiya, tun da yake mun riga mun rantse wa juna da sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji zai zama shaida tsakanina da kai, da tsakanin zuriyarmu har abada.’ ” Dawuda ya yi tafiyarsa, Jonatan kuwa ya koma gari.