1 Samuel 21:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «بَابُ غُرَاسَ إِرِنَّكُواْوَ دَ كُواْوَ، سَيْدَيْ أَݣَويْ غُرَاسَرْ دَ عَكَ ڟَرْكَكٜىٰ؞ ذَاكَ عِيَ طَوْكَ كُثِ عِدَنْ مُتَنٜىٰنْكَ بَسُ ݣُونَ دَ مَاتَابَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗan ya ce wa Dawuda, “Ba ni da abinci don kowa da kowa, sai dai gurasa ta ajiyewa. Zan iya in ba ka muddin dai samarin sun keɓe kansu daga mata.”