1 Samuel 21:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَيَكٜىٰ بَا وَنِ عَبِنْثِ أَوُرِنْ سَيْدَيْ غُرَاسَرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ وَنْدَ عَكَنْ ݣُوشٜىٰ دَغَ غَبَنْ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ عَثَنْجَشِ دَ غُرَاسَ مَيْ ذَاڢِ أَ رَانَرْ دَ عَكَنْ ݣُوشٜىٰشِ، سَيْ ڢِرِسْتِ يَبَا شِ غُرَاسَ مَيْ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗin kuwa ya ba Dawuda tsattsarkan abinci na ajiya, gama ba wani abinci a wurin, sai gurasar ajiyewa kaɗai wadda akan kawar, a sāke sa wata mai ɗumi a ranar da aka kawar da ita.