1 Samuel 21:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَأَمْسَ مَسَ يَثٜىٰ «تَكُواْبِنْ جَالُوتَ مُتُمِنْ ڢِلِسْتِيَ وَنْدَ كَكَشٜىٰ أَ ݣُورِنْ عٜىٰلَ، يَنَ أَنَنْ؞ أَنْ نَطٜىٰشِ دَ ذَانِ عَكَ أَجِيٜىٰ عَبَايَنْ عٜىٰڢُوادْ نَنٜىٰمَنْ نُڢِنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ عِدَنْ كَنَسُواْ كَطَوْكَ، سَيْ كَطَوْكَ؞ شِينٜىٰ كَطَيْ تَكُواْبِنْ دَيَكٜىٰ أَنَنْ؞» دَاوُدَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «أَيْ، بَابُوَنْدَ يَڢِيشِ! كَبَانِشِ حَكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.” Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”