1 Samuel 23:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zifawa suka tafi wurin Shawulu a Gibeya suka ce masa, “Ashe, ba Dawuda ne yake ɓuya a cikinmu a kogwannin duwatsu a Horesh a bisan tudun Hakila, kudu da Yeshimon ba?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْسُ مُتَنٜىٰنْ غَرِنْ ظِڢْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ طَالُوتَ أَ غِبٜىٰيَ سُكَثٜىٰ مَسَ «غَاشِ، دَاوُدَ يَنَ عَٻُواْيٜىٰ عَثِكِنْمُ أَوُرِنْ ٻُيَ نَيَنْكِنْ هُواْرٜىٰشْ عَتُدُنْ هَكِلَ وَنْدَ يَكٜىٰ عَكُدَنْثِنْ يٜىٰشِمُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.