1 Samuel 23:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya tafi Keyila, sai ya ce, “Allah ya bashe shi a hannuna, domin Dawuda ya kulle kansa ke nan da ya shiga birnin da yake da ƙofofin da ake kulle da ƙarafa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَالُوتَ يَسَامِ لَابَرِ ثٜىٰوَ دَاوُدَ يَتَڢِے كَيْلَ؞ دَيَجِ حَكَ سَيْيَثٜىٰ «يَوَّ! اللَّهْ يَسَا شِ أَ هَنُّونَ؞ يَيِ وَكَنْسَ تَرْكُواْ دَ يَشِغَ بِرْنِنْ دَ عَكَ كٜىٰوَيٜىٰ دَ كَتَنْغَ، عَكَ كُمَ ڟَرٜىٰشِ دَ ڧُواْڢُواْڢِنْ دَ عَكَنْ كُلّٜىٰ دَ سَنْدُنَنْ ڧَرْڢٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka faɗa wa Saul Dawuda ya zo Kaila. Sai ya ce, “Madalla, Allah ya bashe shi a hannuna, gama ya kulle kansa, da yake ya shiga garin da yake da ƙofofin da akan kulle da sandunan ƙarfe.”