1 Samuel 24:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، يَوْ كَغَنِ ثٜىٰوَ يَهْوٜىٰهْ يَاسَاكَ أَ هَنُّونَ عَثِكِنْ كُواْغُواْنَّنْ حَرْ مُتَنٜىٰنَ سُكَثٜىٰ إِنْكَشٜىٰكَ، عَمَّا نَڧِ؞ نَثٜىٰ، ‹بَذَنْ مِيڧَ هَنُّونَ إِنْتَٻَ مَيْغِدَانَ بَ، دُواْمِنْ كَيْنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَكٜىٰٻٜىٰ كَذَمَ سَرْكِے؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na ji tausayinka. Na ce, ‘Ba zan miƙa hannuna in kashe ubangijina ba, gama shi keɓaɓɓe na Ubangiji ne.’