1 Samuel 24:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَابَنَ، دُوبِے بَاكِنْ رِغَرْكَ أَ هَنُّونَ؞ دَيَكٜىٰ نَيَنْكِ بَاكِنْ رِغَرْكَ بَنْ كُوَ كَشٜىٰكَ بَ، سَيْ كَسَنِ ثٜىٰوَ بَابُ مُوغُنْ شِرِ غَمٜىٰدَ كَيْ، بَابُ صَاٻُواْ كُواْ وَنِ ذُنُوبِ أَ هَنُّونَبَ؞ عَمَّا دُكْدَهَكَ كَنَ ڧُواْڧَرِ كَكَشٜىٰنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Baba, duba, ga shafin rigarka a hannuna. Tun da yake na yanki shafin rigarka ban kuwa kashe ka ba, sai ka sani ba ni da niyyar yi maka mugunta. Ban yi maka laifi ba, ko da yake kana farautar raina.