1 Samuel 24:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَمَرْ يَدَّ كَرِنْ مَغَنَرْ نَنْ نَدَا يَثٜىٰ، ‹دَغَ مَاسُ مُغُنْتَا مُوغَيٜىٰنْ أَبُبُوَ سُكٜىٰ ڢِتُواْوَ؞› سَبُواْدَ حَكَ، هَنُّونَ بَذَيْ تَٻَكَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.