1 Samuel 25:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَثٜىٰ مُسُ «كُواْوَ يَطَوْكِ تَكُواْبِنْسَ يَرَاتَيَ!» سَيْ دُكْ سُكَ رَاتَيَ تَكُواْبِنْسُ، دَاوُدَ كُمَ يَرَاتَيَ نَاسَ؞ يَطٜىٰبِے مُتَنٜىٰ وَجٜىٰنْ طَرِے حُطُ سُنْ تَڢِے دَشِ، عَمَّا طَرِے بِيُ سُكَ ذَوْنَ سُنَ غَادِنْ كَايَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa ya rataya takobinsa.” Ko wannensu kuwa ya rataya takobi. Dawuda kuma ya rataya nasa takobi. Mutum wajen arbaminya suka tafi tare da shi. Mutum metan kuwa suka zauna a wurin kayayyakinsu.